Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya jagoranci wasu jiga jigan ƴan PDP ɓangaren Ɗarikar Kwankwasiyya zuwa wajen Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari domin komawar su Jam'iyyar APC


Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya jagoranci wasu jiga jigan ƴan PDP ɓangaren Ɗarikar Kwankwasiyya, na tsohon Gwamnan Jihar Kano Engr. Rabiu Musa Kwankwaso zuwa wajen Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari domin komawar su Jam'iyyar APC.
Waɗanda ya jagoranta sun haɗa da tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Farfesa Hafizu Abubakar, Akitet Aminu Dabo, Bala Mohammed Gwagwarwa, Janar Idris Bello Dambazau (rtd); Engr. Mu’azu Magaji da kuma Sanata Isa Yahaya Zarewa a ɗaya gefen.
Gwamna Badaru shi yayi ƙoƙarin janyo hankalin su dawowa Jam'iyyar inda ya samu nasarar ɗaukar su zuwa Abuja a daren jiya domin ganawa da Maigirma Shugaban Ƙasa.
Auwal D. Sankara (Fica),
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)

Post a Comment

Previous Post Next Post