UMAR MAKAMA GALAMAWA YA DAWO APC


UMAR MAKAMA GALAMAWA YA DAWO APC
Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya karɓi baƙuncin Umar Makama Galamawa a ofishin sa a yau.
A kwanakin nan ne Umar Makama ya shiga Jam'iyyar PDP amma yayi komayya zuwa Jam'iyyar APC saboda cewa da yayi ya fahimci aƙidun Jam'iyyar PDP bata dace da nasa aƙidar da aƙidar talakawa ba.
A yayin da yake karɓan sa, Gwamna Badaru ya masa maraba da dawowa gidan sa na asali, inda yace Jam'iyyar APC zata iya baiwa kowa matsuguni tare da alƙawarin aiki da duk waɗanda suke da aniyar dawowa.
Auwal D. Sankara (Fica),
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)
21/12/2018

Post a Comment

Previous Post Next Post