Maigirma Matar Gwamnan Jihar Jigawa Hajiya Magajiya Muhammad Badaru Abubakar ta ƙaddamar da shirin rabon tallafi na jarin ₦5, 000 ga mata goma a kowane akwatu.
Ƙaddamar da shirin wanda aka gudanar a Ƙananan Hukumomi 8 na yankin Sanata na Jigawa na Arewa maso Gabas, wanda zai tallafawa mata 9, 720 a akwatunan zaɓe 9,720 cigaban shirin ne da aka faro daga Ƙananan Hukumomin Gumel da Sule Tankarkar wanda uwargidan Maigirma Gwamnan Hajiya Hasinah ta ƙaddamar wanda mata 2, 200 suka ci moriyar shirin.
Daga fara ƙaddamar da shirin a watannin baya, adadin mata 11,920 ne daga akwatunan zaɓe 1, 192 polling suka karɓi tallafin da ya kai na kimanin Naira Miliyan N59.6M.
Shirin zai cigaba da gudana har sai an karaɗe akwatunan zaɓe 3,527 na faɗin jihar, inda mata 35,270 zasu ci gajiyar shirin wanda ake sa ran za a raba kuɗaɗe kimanin Naira Miliyan N176, 350 a faɗin jihar.
A yankin Hadejia kaɗai, kimanin Naira Miliyan 48.6 ne za a rabar.
Auwal D. Sankara (Fica),
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)
Tags:
Jigawa state APC
