GWAMNA BADARU YA SAMU LAMBAR YABO DAGA MANOMA SHINKAFA BA ƘASA


GWAMNA BADARU YA SAMU LAMBAR YABO DAGA MANOMA SHINKAFA BA ƘASA
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bawa Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar lambar yabo a yayin taron karramawa na Ƙungiyar Manoma Shinkafa na Ƙasa wanda aka gudanar a ranar 19 ga watan Disamba 2018 a Birnin Tarayya, Abuja.
Haka nan an karrama Gwamnan Jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele.
A yayin taron an kuma karrama Shugaba Muhammadu Buhari da lambar yabo wanda Shugaban Manoma Shinkafa na Kasa Alhaji Aminu Goronyo ya miƙa masa.
Auwal D. Sankara (Fica),
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)

Post a Comment

Previous Post Next Post