kwamishinan yan sanda na kasa ya gargadi yan kasuwa da su daina ba yan sanda bashi


Ku daina ba yan sanda bashi - Kwamishinan Yan sanda ya gargadi yan kasuwa

Kwamishna 'yan sandan jihar Kwara, Fafowora Bolaji, ya shawarci jama'ar Jimba Oja da su guji sayar da kayansu ga jami'an 'yan sanda a kan bashi.
.
Bolaji ya ce bawa jama'ar wannan shawara ya zama domin gudun fadawa cikin mawuyacin hali yayin da aka yiwa jami'in da suka bawa bashi canjin wurin aiki.
.
Ya bayar da shawarar ne ranar Lahadi yayin taron bikin bude karamin ofishin 'yan sanda a Kamwire dake Jimba Oja, da kamfanin KAM suka gina.
.
Kar ku sake ku sayar da kayanku bashi ga jami'an 'yan sanda saboda za a iya yi masa canjin wurin aiki a kowanne lokaci," a cewar Bolaji.
.
Kazalika, kwamishinan ya mika godiya ga kamfanin da ya gina ofishin 'yan sandan tare da yi masu albishir din cewar zai tabbatar hukamar 'yan sanda reshen jihar Kwara tayi amfani da ofishn domin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyar al'ummar yankin.
.
A nasa jawabin, Dakta Kamaruddeen Yusuf, shugaban kungiyar masu masana'antu a jihar Kwara da Kogi, ya bayyana shigar jama'a harkokin tabbatar da tsaro da abu mai matukarmuhimmanci.

Post a Comment

Previous Post Next Post