Rawar da gwamnan jihar katsina Rt Hon Aminu Bello masari ya taka a fannin ilimi


MATAWALLEN HAUSA DALLATU
!
Rt Hon Aminu Bello masari Gwamnatinsa tataka muhimmiyar rawa wajan ganin an inganta Harkar Ilimi ajihar Katsina da kEwaye.
!
ILIMI:
A fili yabayyana cewa' babu wata al'umma da za ta daukaka takuma samu cigaba face sai sunkasance masu ilimi.
!
Wannan dalilin ya sanya gwamnatin Gwamna Masari har gobe take sanya harkar ilimi a mataki na daya, na biyu da na uku a cikin gwamnatin na shi, wanda hakan ne ya
sanya a cikin shekarun nan Hudu, sashen na ilimi ya lamushe akalla kashi 22 na duk kudaden kasafin kudinta na shekara.
!
Gwamnatin Masari tayi kokari a sashen na ilimi, musamman a makarantun Firamare da Sakandare, wanda hakan yahabbaka harkar ilimi.
!
Wannan kokarin tallafawa harkar ilimi da gwamnatin Masari ta
yi a sashen na ilimi bai takaitu a samar da gine-gine kadai ba, ya hada har da horas da su kansu malaman makarantun da ingantaccen ilimi.
!
kuma Gwamnatin masari ta kara daukan
wasu kwararrun malaman, kuma ta kyautata masu, tayi masu karin girma da kuma biyan su albashin su da sauran hakkokinsu a kan lokaci.
!
A baya, muna da azuzuwan karatu ne da aka gina su domin daukan dalibai 50, amma sai ya kasance
ana cusa masu dalibai har sama da 150, a
makarantun Firamare da kuma na Sakandare, nan
da nan gwamnatin Masari ta dukufa wajen gyarawa da kuma gina sabbin ajujuwan ta yanda har aka kai
ga samar da sabbin ajujuwa 752 acikin shekaru 3, aka kuma gyara sama da guda 1,598, a duk fadin Jihar Katsina.
!
Aka kuma
samar da ababen zama da na karatu sama da guda 10,000, da suka hada da kujeru da tebura masu dauke da mazaunae biyu duk an samar da su kuma
tuni an rarraba su. #Mayen Apc
!
Hakan ya sanya masu mallakan makarantu masu zaman kansu na kuka da cewa ana kwashe masu dalibai, domin kuwa a yanzun iyaye sun gwammace
su kai ‘ya’yansu makarantun Firamare da
Sakandare na gwamnati da suke a garuruwan
Katsina da Daura.
!
Hakanan kuma an samar da dakunan gwaje-gwaje na kimiyya da fasaha daidai da zamani da dakunan karatu na zamani, gami da yadda aka adanta ajujuwan da Kwamfutoci, wadanda ba za ka taba samun kwatankwacin su a
dukkanin makarantu masu zaman kansu ba a Jihar Katsina.
!
A jimlace, gwamnatin ta Masari, ya zuwa yanzun ta gyara gami da gina sabbin makarantun Firamare 160 da kuma na Sakandare 25, da suka hada da gina ajujuwa, da dakunan kwana a makarantun
Sakandare na kwana a kowane daga cikin mazabun dan Majalisar Dattawa uku na Jihar.
!
Gwamnatin ta yi karin girma tare da biyan kudaden ariyas na Malaman Firamare da Sakandare sama da 1100 a Jihar, wasu daga cikinsu sun shafe sama da shekaru 10 ba tare da samun karin girman ba.
!
Dukkanin Makarantun mata a yanzun sun zama na kwana.
Tare da malamai sama da 2000 da ake da su a
makarantun na Firamare da Sakandare, a yanzun
haka muna shirin kara daukan wasu 5000 ne sabbi a karkashin shirin S Power.
#KatsinaMedia
!
HARKAR ILIMI TAXAMA ABUN ALFAHRI AJIHAR KATSINAWA AIKI KAWAI BABA MASARI.

Post a Comment

Previous Post Next Post