sakon sabuwar shekara da gwamnan jihar jigawa ya fitar




NEW YEAR 2019 MESSAGE FROM GOVERNOR BADARU 
The Governor of Jigawa State Alhaji Muhammad Badaru Abubakar wishes to felicitate with the people of Jigawa state and other Nigerians as the country moves into the year 2019 and said that the year 2019 will offer better and greater opportunities.
Governor Badaru said that the year 2019 will be a blissful year to all Nigerians as the change mantra of President Muhammadu Buhari will manifest more if re-elected and call on Nigerians to continue supporting the administration and give President Muhammadu Buhari and all APC Candidates in the next general elections another chance, as it is now obvious that APC change mantra has taken root in every sector of the economy and security and will refine our value system that will bring about the desired development for the people of the country when the party candidates are given another chance.
He urged the people of Jigawa State in particular and Nigeria in general to take advantage of the policies of the APC administration and assures them of more in 2019.
Governor Badaru reaffirms the assurance of his administration to uphold transparency, accountability, as well as investing on citizenry by empowering them as demanded by the change mantra.
The Governor wishes Jigawa people and Nigerians a prosperous New Year 2019.
**************************************************
SAKON MURNAR SABUWAR SHEKARA DAGA GWAMNA BADARU 
Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar yana taya ɗaukacin Al'umar Jihar Jigawa da sauran ƴan Najeriya murnar shiga Sabuwar Shekarar 2019, inda yace shekarar 2019 zai kasance mai cike da nasara da ƙarin sabbin damammaki ga al'umar Ƙasar nan.
Gwamna Badaru yace shekarar 2019 zai zama mai tarin alheri ga ƴan Najeriya kasancewar canjin da Maigirma Shugaban Ƙasa ya kawo zai cigaba da wanzuwa musamman idan ƴan Najeriya sun ƙara bashi dama na ƙara zaɓan sa da sauran ƴan takarar Jam'iyyar APC a babban zaɓe mai zuwa, bisa la'akari da canji ya tabbata a dukkan ɓangarorin tattalin arziki da tsaro, wanda hakan zai cigaba da tabbata ne inda an ƙara bawa ƴan takarar Jam'iyyar wata dama.
Gwamnan yayi kira ga al'umar Jihar Jigawa da sauran ƴan Najeriya suyi amfani da suke da shi da Jam'iyyar APC ta samar musu tare da yi musu alƙawarin ƙarin wasu tagomashin a Shekarar 2019.
Gwamna Badaru ya kuma tabbatar da burin gwamnatin sa na aiki da gaskiya, tsantseni da kuma tallafawa al'uma, wanda suna cikin manufofin Jam'iyyar APC.
Gwamnan yana taya al'umar Jihar Jigawa da sauran ƴan Najeriya murnar Sabuwar Shekarar 2019 da fatan Allah yasa mun shiga a sa'a.
Auwal D. Sankara (Fica), 
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media 
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)
01/01/2019

Post a Comment

Previous Post Next Post