Gwamnatin jihar Katsina ta lashi takobin inganta tsaro


ANIYADAI MAQIYA MAZA BISA KANKU
!
#Mayen Apc
Gwamnatin jihar Katsina ta lashi takobin inganta tsaro sosai, ta hanyar kara wa yan bangar jihar Katsina kayan aiki sosai domin kawo tsaro mai inganci a duk fadin jihar Katsina.
!
Gwamnan jihar Katsina H.E Aminu Bello Masari ya bayyana haka, a ta bakin wakilinsa kuma
sakataren gwamnatin jiha Dr Mustapha Inua da ya karbi bakuncin tawagar yan bangar da
suka kai ziyarar ban girma da jinjinawa gwamnatin jihar Katsina a gidan gwamnati dake gidan Muhammadu Buhari.
!
Tun da farko dai shugaban tawagar yan bangar Abdullahi Lolo, shi ne ya bayyana wa gwamnatin jihar korafe-korafensu a kan rashin kayan aiki, irinsu motoci, da kwari da baka, gorori, da sauran kayan aikin da za su taimaka masu wajen inganta tsaro.
!
Daga karshe Dr Mustapha Inua, ya jinjinawa masu a kan yadda suke kokari wajen taimakawa wajen samar da tsaro a cikin jihar, tare da shan alwashin
gwamnati za ta taimaka masu da kayan aiki, isassu ba tare da bata lokaci ba.
#KatsinaMedia
!
Allah yaqara Taimakawa Gwamna masari da mukarrabansa katsinawa godiya muke .
!
MASARIYYA BUHARIYYA
4+4 INSHA ALLAH

Post a Comment

Previous Post Next Post